Posts

Showing posts from August, 2019

(3): Tambihin wasan kwaikwayo: Timeless; Ɗanɗanon Zarrar Abinda fasahar Gobe Ta ƙunsa.

Image
Wannan Tambihi ( Review ) na rubutashi musamman don murnar zagayowar ranar Hausa, wato 26 ga watan Agustan shekarar dubu biyu da sha tara miladiyya. Tun wajen farkon ƙarni na sha tara dai masana kimiyya da fasahar ƙasar birtaniya suka ƙera abinda muke kira "inji". Wanda babu jimawa kuma aka samu wasu masana fasahar suka ƙera na'ura mai ƙwaƙwalwa, jirgin sama, wanda a cikin ƙarni na ashirin har da makamashin nukiliya, wayar hannu da kuma yanar gizo-gizo. Wannan kaɗan ne daga cikin manyan ƙere-ƙere da masana, da kuma masu fikira suka aiwatar. Toh amma, a yanayin yadda takun fikirar masana kimiyya da fasaha ke cigaba kullum, an samu har sun ƙera saƙago na na'ura a cikin ƙarni na ashirin da ɗaya, wanda hakan ya janyo tambayar, shin idan har saƙago zai iya ƙeruwa yayi aiki kamar mutum, shin menene matakin ƙarshe na zarra da kimiyya da fasaha zata kai a nan gaba kuma? Wasan kwaikwayo na Timeless dai labari ne da ya bamu leƙen asiri akan abinda gobe zata iya h...