(3): Tambihin wasan kwaikwayo: Timeless; Ɗanɗanon Zarrar Abinda fasahar Gobe Ta ƙunsa.



Wannan Tambihi (Review) na rubutashi musamman don murnar zagayowar ranar Hausa, wato 26 ga watan Agustan shekarar dubu biyu da sha tara miladiyya.

Tun wajen farkon ƙarni na sha tara dai masana kimiyya da fasahar ƙasar birtaniya suka ƙera abinda muke kira "inji". Wanda babu jimawa kuma aka samu wasu masana fasahar suka ƙera na'ura mai ƙwaƙwalwa, jirgin sama, wanda a cikin ƙarni na ashirin har da makamashin nukiliya, wayar hannu da kuma yanar gizo-gizo. Wannan kaɗan ne daga cikin manyan ƙere-ƙere da masana, da kuma masu fikira suka aiwatar.

Toh amma, a yanayin yadda takun fikirar masana kimiyya da fasaha ke cigaba kullum, an samu har sun ƙera saƙago na na'ura a cikin ƙarni na ashirin da ɗaya, wanda hakan ya janyo tambayar, shin idan har saƙago zai iya ƙeruwa yayi aiki kamar mutum, shin menene matakin ƙarshe na zarra da kimiyya da fasaha zata kai a nan gaba kuma?

Wasan kwaikwayo na Timeless dai labari ne da ya bamu leƙen asiri akan abinda gobe zata iya haifarwa a duniyar kimiyya da fasaha, wanda kamfanin fina-finai na Sony pictures Television da Universal television suka ƙir-ƙira, wanda kamfanin akwatun kallo na NBC suka ɗauki nauyin gabatar dashi. Manyan masu bada umarni Shaw Ryan, John Davis da Neil Marshal, ne suka bada da umarni. Su kuma Bard Van Arragon da Shawn Williamson ne suka ɗauki nauyi. An fara fitar dashi a watan Oktobar shekarar dubu biyu da sha shida miladiyya, har zuwa ashirin ga watan Disambar shekarar dubu biyu da sha takwas miladiyya.

Labarin Timeless an gina shi akan labarin wata masana'antar ƙere-ƙere da ake kira 'mason industries', mallakar wani ba-amurke baƙar fata, da ake kira Conor Mason. Malam Mason dai yayi aiki tuƙuru shi da ma'aikatan kamfanin sa wajen ganin sun ƙera inji wanda zai bawa ɗan adam ikon yin bulaguro zuwa kowanne lokaci, wanda zai zo da kuma wanda ya wuce, wanda ake kira da "Time Machine" a turance, wanda sun aiwatar da hakan cikin nasara. Kuma kasantuwar wannan ƙira ta musamman sabuwa, kuma irinta ta farko, ya janyo hankalin duniya kanta, wanda har kafin masana'antar Mason ta farga, an samu wani ɗan sababi mai suna Garcia Flynn, ya sace wannan inji, ya kuma gudu dashi zuwa shekarar 1937, dai-dai lokacin da haɗarin fashewa zai afku a cikin sunduƙin tafiye-tafiye yayin da yake komawa zuwa nahiyar turai, don halartar naɗin sarautar sarki George na shida, mahaifin sarauniya Elizabeth ta biyu dake birtaniya. Fatan Garcia Flynn shine yaje ya canza yadda wannan haɗari ya faru, kamar dai yadda ta faru a cikin tarihi, domin hana faruwar wasu abubuwa da suka faru a tarihi, sakamakon fashewar wannan sunduƙi.

Babbar hikimar Garcia flynn da ta janyo ya sace "Time Machine" shine yayi wa tarihi garambawul. Wanda a fuskantata, yayi amfani da karin maganar larabawa da Mal. Abubakar Imam ya ambata a cikin littafin sa na Ruwan Bagaja, wato: "Qatala muzi qabla an yuzi ka". Bi ma'ana: " Ka kashe makashin ka tun kafin ya kashe ka". Flynn yana so yaje yaga bayan duk wani abu da ya kawo wa soye-soyen zuciyar sa a tarihi tsaiko, tun kafin hakan ya afku. Misali, idan mace mai ciki ta mutu yayin haihuwa, ma'ana juna biyu ne yayi ajalin ta, wanda hakan na nufin da bata sami juna biyu ba, bazata mutu ba. Toh don gudun kada ta mutu, me zai hana aje a hanata samun wannan juna biyu. Garcia yana ganin idan yaje ya hanata haɗuwa da mutumin da zata samu juna biyu tare dashi, hakan zaisa ba zata taɓa samun juna biyu ba, sai kuma ya sanya ta rayu har zuwa lokacin da Garcia yake so takai a cikin tarihi. Toh fa!

Wannan tunani na Garcia ba komai bane illa juyin-juya hali na yiwa tarihi ta'addanci. Wanda idan aka zuba masa ido, zai yiwa tarihi kaca-kaca, ya maidashi yadda ransa yake so. Sabili da haka, kamfanin Mason da haɗin gwiwar hukumar bincike ta Amurka wato FBI, suka gayyaci farfesar tarihi 'Lucy Preston' da jarumin soja 'Wyatt Logan' da masanin na'ura, wato: "Rufus carlin" baƙar fata kuma mutum na biyu da shi kaɗai ya iya tuƙin 'Time Machine' bayan direban da Garcia Flynn ya sace., akan su shiga cikin injin ko ta kwana da aka ƙirƙirarwa shi wannan "Time machine" saboda rana irin wannan, su bi bayan Garcia Flynn, su kamo shi tun kafin ya aikata ɓarna.

Fasahar sanya farfesar tarihi Lucy Preston ta ja ragamar kamen Garcia shine daga ƙarni na sha huɗu, har zuwa ƙarni na ashirin da ɗaya babu wani muhimmin al'amari da ya faru a doron ƙasa wanda Lucy Preston bata san waye ya haddasa shi ba, da mutanen da suka aiwatar dashi, da kuma hanyoyin da akabi aka magance shi. Daɗin daɗawa kuma da yanayin al'adu na rayuwar mutane dake canjawa akan lokaci ya sanya dole sai da wanda yasan yadda al'adun baya suke. Don haka ita ce tasan me Garcia Flynn zaije yi, idan na'urar bin sahu wato 'Tracker' ta 'Time Machine' ta nuna yayi tafiya zuwa wata shekara a baya, don tana da masaniya akan duk wasu muhimman lamurra da suka afku, masu alaqa da son zuciyar Flynn, da kuma irin yanayin matakan da ya kamata su ɗauka na yanayin sanya suttura, yare, da sauran su yayin da suka bi bayan sa. Wyatt Logan ya shiga sahun mabiya bayan ƙeyar Garcia Flynn domin yiwuwar tashin zaune tsaye, wanda a matsayin sa na ƙwararren soja, yana da gogewar da zai kula da duk wani yamutsin gwada ƙwanji da ka iya tasowa. Shi kuma Rufus Carlin direba ne, kuma bakaniken 'Time Machine'.


  • Manyan darussan tattaunawa:



  • Wasan kwaikwayo na Timeless wasa ne mai matuƙar burgewa, mai cike da al'ajabi da kuma ban mamaki, wanda zai cika zuciyar ɗan kallo da tambayoyi da dama. Mafi burgewa daga wasan shine yadda wasan zai tayarwa da duk wani ɗan kallo mai son ji da kuma karanta tarihi sha'awar komawa ya bibiyi tarihi. Domin sanadiyyar yunƙurin Garcia Flynn na son yiwa tarihi garambawul, da kuma yadda ma'aikatan Mason suka bi bayan sa, ya sanya wasan ya nuna muhimman al'amura da suka faru a cikin tarihin Amurka. Misali, a fai-fai na biyu, Garcia Flynn ya tuƙa "Time machine" zuwa ashirin da shida ga watan afrilun shekarar 1865, wanda yayi dai-dai da ranar da aka kashe limamin dumukuraɗiyya, kuma shugaban Amurka na sha shida a tarihi, mai ci a wancan lokaci, wato Abraham Lincoln. Fasahar Garcia ta zuwa wannan lokaci shine ya tabbatar da manyan masu iko na cikin gwamnatin Lincoln - Frederick Seward, William H. Seward, da Andrew Johnson, wanda tarihi ya nuna sun tsira lokacin harin kisan kan da aka aiwatar a gidan kallon wasa na "Ford" dake washington DC, cewa suma sun mutu. Dalilin da ya sanya shi yin hakan kuma shine, ɗaya daga cikin mutanen nan, zai kafa wata ƙungiya a gaban wancan lokaci, wadda zata ɗau nauyin kisan matar sa. Wanda ida ya tabbata sun mutu, to bazasu rayu su kafa waccan ƙungiya ba, wanda hakan zai magance mutuwar matarsa a zamanin da muke ciki. Kamar dai karin maganar hausawa dake cewa: "Rigakafi yafi magani".


Flynn Baiyi nasara ba, amma ya tabbatar da mutuwar Abraham Lincoln, ta hanyar aiwatar da kisan da kansa. Yayin da su kuma Lucy Preston, Wyatt Logan, da Rufus Carlin suka tseratar da wannan mutane daga sharrin Garcia Flynn. Wani babban al'amarin shine, a asalin tarihi, wannan mutane sun samu raunuka. Amma zuwan su Lucy da Wyatt da Rufus, sai suka sanya basu samu raunuka ba, wanda haka ya canja tarihi kenan, kuma zai murɗa yadda wasu lamurra suke a zamanin da muke ciki, tunda abinda ya faru a zamanin baya, shi ya ke haifar da abinda ke faruwa a wannan zamani. Bayan Flynn yaƙi kamuwa a wancan lokaci, sai su Lucy suka tuƙo injin su zuwa asalin zamanin mu, inda anan suka tarar da abin ban mamaki. Lucy dai ta samu mahaifiyar ta dake kan gadon asibiti ba yadda take, lafiya sarai, nuni da cewa bata taɓa ciwo irin wannan ba a rayuwar ta. Sannan kuma ta tarar cewa mahaifinta ba shine mahaifin ta ba, kuma iyayen ta ita kaɗai suka haifa, wanda kafin ta tafi kamen Garcia, duk ba haka bane, amma kuma yanzu duk sun canza. Meye dalili? Hana manya a gwamnatin Lincoln samun rauni yayin harin kisan kai, shi yaje ya dawo ya canza tarihi, wanda ita ma ya shafeta. Turƙashi! Hakan ya sanya suma suka so su sami damar yin amfani da "Time machine" domin komawa baya su maida tarihin su dai dai. Da sauran su. Timeless yana cike da tarihin amurka, tun daga kan George Washington, har zuwa kan Ronald Reagan, da abubuwa muhimmai da suka afku a lokutan.


  • Wasan kwaikwayo na Timeless, kamar dai sauran wasannin kwaikwayo, ya shiga tarkon ƙauna, wanda a sauran tambihaina na turanci na kira da "extreme love circle". Gaba ɗaya abinda Garcia Flynn ya aiwatar, ya aiwatar ne saboda matarsa, abar ƙaunar sa, ta dawo da rai. Wanda sanadiyyar haka, Lucy ta rasa ƴar uwarta abar sonta, kuma tayi yunƙurin ta dawo da ita. Shima kuma Wyatt Logan, yayi yunƙurin ya dawo da hasken ransa, matarsa da ta mutu. Wanda shima kuma Rufus, ya haɗu da abokiyar aikin sa 'Jiya', matashiyar yarinya mai kyawun ban mamaki, wanda ta kusa rasa rayuwarta, wanda hakan ya tunzura Rufus, kuma ya ƙara kyautata salon wasan kwaikwayon baki ɗaya. A taƙaice, ƙauna tayi bulaguro da na'urar bulaguron zuwa lokaci.



  • Shin "Time Machine" ko kuma "Time travel" zai iya faruwa? Wannan babbar tambaya ce, wanda nima nayi ta tambayar kaina, da kuma sauran masana ilimin kimiyyar lissafi (Mathematics), da kuma kimiyyar nazarin azancin yadda maganaɗisan doron ƙasa ke gudana (Physics). Wasan kwaikwayon Timeless ya nuna ƙarfin fikirar masana kimiyyar lissafi, amma kuma babu wani cikakken nuni akan yiwuwar "Time machine" ta mahangar kimiyyar doron ƙasa (Physics). Me yiwuwa tunda shi lissafi abune da ya taɓa komai (General), shi kuma kimiyyar doron ƙasa (physics) abu ne da iyaka doron ƙasa ya taɓa (specific universe), me yiwuwa "Time Machine" da kuma "Time Travel" ya yiwu ta mahangar lissafi, amma kuma ba komai ne yake me yiwuwa ta mahangar lissafi wanda zai yiwuwu ta mahangar kimiyyar lokaci, da azancin faruwar abubuwa a doron ƙasa, wato (physics). Koma dai menene, saura ya rage ga masana


Amma kuma a zafin taku irin na kaifin fasahar bincike, da kuma yadda komai yake cigaba a hankali, alaƙa da duba da yadda shaihin tarihi, kuma mai hasashen abin da ka iya faruwa a zamanin da muke ciki da kuma wanda zaizo, farfesa Yuval Noah Harari, ya hasaso cewa rayuwa har abada babu mutuwa (immortality) zai zamo abinda ɗan adam zai karkata binciken sa akai, wanda idan hakane, tsawaita bincike akan bulaguro zuwa lokaci bazai zama abin mamaki ba, idan har za'a yadda a kuma fuskanci abinda Harari yace. Duk da yake, so samu, wasan kwaikwayo ya kasance abinda bai zarce hankali ɗan kallo ba, ko kuma abinda zai iya yadda.


  • A ƙarshen shirin Timeless, duk mai neman wata amsa, ko kuma mai neman juya wani abu a cikin tarihi, yayi iya yin sa, amma kuma komai ya zauna yadda yake, idan aka cire ƙananun saɓani da ba'a rasa ba. Wannan mai yiwuwa yana nuni da cewa akwai wani abu wanda yafi ƙarfin kimiyya da fasaha, wanda yafi ƙarfin juyin mai fasaha ko kuma wani abu makamanci. Wannan abu ba komai bane illa "ƙaddara". Wadda dole kowa ya haƙura ya rungumeta yadda tazo. Komai zaije ya dawo, amma ƙaddara tana nan tana jira, kuma komai sai ya taras da ita.


A ƙarshe, shirin Timeless shiri ne da tsayawa yabon yadda aka tsarashi zai zamo kamar ɓata lokaci, domin yadda labarin ya shiryu, da yadda jaruman shirin suka taka rawar gani, abun ba'a cewa komai. Ƙagaggen shirine akan kimiyya da fasaha ( Science fiction), wanda ya ginu bisa ganuwar tarihi (History), da kuma ya bamu ɗanɗanon zarrar kimiyya a lokacin da muke ciki, da ma wanda zai zo. Ina bawa duk wani mai son tarihi shawarar ya kalli shirin "Timeless". Hakana duk mai son kallon fina-finan kimiyya da fasaha, da kuma shiryayyun wasannin kwaikwayo da suke ɗauke da salon magana masu ɗaukar hankali, da ƙarfi irinna na yaren turanci. An shirya faya-fayen sa a tsarin tarago-tarago (Episodes), kuma an ƙare shi a shiryawa ta biyu (Season 2). Na bashi maki 8 a cikin 10: 8/10.

Mai tambihi:
MA Iliasu
Kano State, Nigeria.

Email: Muhada102@gmail.com
Twitter: @MA_Iliasu
Facebook: MA Iliasu

Comments

  1. Wow it’s very interesting my uncle Allah yaqara basira ����

    ReplyDelete

Post a Comment