Posts

Showing posts from March, 2023

(44); ME YASA KANAWA MUKA ZAƁI ƘWANKWASO A ZAƁEN SHUGABAN ƘASA DUK DA MUN SAN BA ZAI CI BA?

Ga mutane gama-gari wanda ba su da komai face ƙawa-zuci, ra'ayi kaɗai ya isa dalilin zaɓa ko ƙin zaɓar kowanne ɗan takara. Amma ga mutanen da abinda ake zato daga gare su ya kere ƙawa-zuci, buƙatar yanke shawara a gwanance domin cimma wata manufa ya zamo kamar wajibi ne a mahanjar al'umma masu kamanceceniyar addini, al'adu, wurin zama da kishin juna kamar tamu ta Arewacin Najeriya. Da Dr. Rabi'u Kwankwaso ya fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar NNPP a zaɓen Fabrairun 2023, yawancinmu mun san cewa fandishon jam'iyyar NNPP bai kai taci kujerar shugaban ƙasa ba. Hasalima Atiku Abubakar zai fi jam'iyyar samun yawan ƙuri'u. Idan kuma haka ne, zaɓar jam'iyyar, ko kuma kira da a zaɓi jam'iyyar, ai ya zama daidai da sanya jari a bankin asara kenan. Ko ba haka ba? Amma inda gizo ke saƙar shine, Kanawan Dabo sun zauna sun yi karatun ta natsu. Daga hakan kuma muka iya gano cewa jagora Kwankwaso yayi nazarin wasu daga cikin dalilan da suka janyo s...

(43); Kamar Kwankwaso kamar Caliph al-Mahmūn.

MA Iliasu Ƙasa da shekaru maitan bayan hijira daga Makkah zuwa Madinah, za'a ci karo da wani mashahurin shugaba mai suna al-Mahmūn wanda yayi kalifancin daular Abbasawa a birnin Bagadaza. Duk da cewa ana ambaton shugabanni irinsu Umar Bn Abdulaziz, Abdulmalik Bn Marwan da Harūn al-Rashid a farko a fagen mulki da siyasar daula, idan tattaunawa akan malalowar ilimin kimiyya ne da falsafa cikin daular musulunci, sunan al-Mahmūn ne yafi fitowa fili. Misali: Dr. Abdul'azim Islahi ya kambama shi a matsayin wanda ya sanya aka fassara ilmomin Girkawa, Farisawa, Indiyawa da Sinawa zuwa yaren larabci don masu nazari su amfana. Ibn Khaldoun kuwa cewa yayi duk wani Ilimin kimiyya da aka neme shi aka rasa a bainar musulmi, an rasa shi ne kaɗai saboda al-Mahmūn bai fasssara shi ba - saboda tsabar tasiri kenan. Da aka matsa gaba zuwa ƙarni na sha ɗaya kuwa, har zuwa ƙarshen ƙarni na sha biyu miladiyya, lokacin da Mongoliyawa suka fara kawo farmaki daular musulmi, sai ya kasance tattaunawa aka...