(44); ME YASA KANAWA MUKA ZAƁI ƘWANKWASO A ZAƁEN SHUGABAN ƘASA DUK DA MUN SAN BA ZAI CI BA?
Ga mutane gama-gari wanda ba su da komai face ƙawa-zuci, ra'ayi kaɗai ya isa dalilin zaɓa ko ƙin zaɓar kowanne ɗan takara. Amma ga mutanen da abinda ake zato daga gare su ya kere ƙawa-zuci, buƙatar yanke shawara a gwanance domin cimma wata manufa ya zamo kamar wajibi ne a mahanjar al'umma masu kamanceceniyar addini, al'adu, wurin zama da kishin juna kamar tamu ta Arewacin Najeriya.
Da Dr. Rabi'u Kwankwaso ya fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar NNPP a zaɓen Fabrairun 2023, yawancinmu mun san cewa fandishon jam'iyyar NNPP bai kai taci kujerar shugaban ƙasa ba. Hasalima Atiku Abubakar zai fi jam'iyyar samun yawan ƙuri'u. Idan kuma haka ne, zaɓar jam'iyyar, ko kuma kira da a zaɓi jam'iyyar, ai ya zama daidai da sanya jari a bankin asara kenan. Ko ba haka ba?
Amma inda gizo ke saƙar shine, Kanawan Dabo sun zauna sun yi karatun ta natsu. Daga hakan kuma muka iya gano cewa jagora Kwankwaso yayi nazarin wasu daga cikin dalilan da suka janyo suɓucewar kujerar gwamna a zaɓen 2019. Kuma muhimmi daga ciki akwai kasancewar yadda har yanzu a tafiyar Kwankwasiyya babu wani ƙusa da yake da rabin tasirin Madugun da kansa. Dalilin haka kuma ha sanya janyewa gefe da Madugun yayi, yaƙi fitowa takarar komai a zaɓen 2019, ya ragewa jama'ar Kano karsashin dangwalawa ƴan takarar da suka dace. Hakan kuma ya bawa ɓata gari damar suka aikata abinda suka aikata.
Wani ƙarin jidalin kuma shine, bayan da APC ta ƙwace zaɓen 2019, sai ya kasance an yiwa siyasar Kano kisan mummuƙe, an shigo da wata siga ta mugunta wadda zata gurgunta duk wani tubali da mashahuran ƴan siyasar jihar Kano na baya suka kafa. Wanda kuma idan aka bari suka mamaye jihar a zaɓen 2023, siyasar Kano zata shiga halin ha'ula'i na har abada. Kuma domin ceto jihar, tilas jagora Kwankwaso da ƙusoshinsa da al'ummar Kano su ci alwashi kuma su samu matsaya akan aiwatar da abinda ya dace.
Hanya ta farko da za'a fara bi domin tayar da waccan komaɗa itace ta hanyar tabbatarwa da jama'ar Kano cewa Madugu yana nan da rai bai mutu ba. Hakana abinda ya faru a 2019 tsautsayi ne irin na siyasa. Domin aiwatar da hakan kuma tilas ya fito takarar shugaban ƙasa. Ta hakan Bakano zai san cewa har yanzu akwai wani tubali mai isasshen ƙwarin da duk mutanen Kano zasu iya dogara da shi.
Ranar da jagora Kwankwaso ya shigo garin Kano domin "campaign" na ƙarshe itace ranar da Bakano ya sallama cewa haƙiƙa siyasar Kano bata mutu ba. Kuma tabbas jagora Ƙwankwaso da muƙarabbansa a shirye suke domin ceto jihar. Mu ganau ne, ba jiyau ba. Saboda mutane da dama da suka yi ridda irinta siyasa sun tuba a ranar. Domin gane hakan kuwa, shin zamu iya tuna a gaba ɗaya zaɓen 2019 ƴan majalisar tarayya da sanatoci guda nawa Ƙwankwasiyya ta samu? Amma yanzu a 2023 guda nawa ta samu?
Bambancin shine a 2019 Ƙwankwaso bai fito takarar komai ba, amma a 2023 ya fito takarar shugaban ƙasa. Wato dai kafin Bakano yaji karsashin yin zaɓe, yana buƙatar yaga sunan Madugu akan takardar INEC. Gane hakan kuma yasa Madugun ya fito takara duk da ya san ba zai ci ba, kawai don ya ƙarfafawa jama'a gwiwar su fito suyi abinda ya dace.
Idan aka juyo gare mu kuma, ƴan kwankwasiyya, mun yi rubututtuka da yawa domin hilatar jama'a su zaɓi Ƙwankwaso a zaɓen shuagaban ƙasa duk da cewa mun san lokacinmu bai zo ba. Wasu daga ciki sun janyo mana zagi. An kira mu wawaye. Wasu sunce sun raina wayonmu. Saboda muna ajiya a bankin hasara. Amma abinda basu gane ba shine, dalilinmu na yin hakan shine mun gano cewa yawan mutanen da suka yi imani da cewar Ƙwankwaso zai iya cin shuagaban ƙasa zai yi daidai da yawan mutanen kirkin da za'a zaɓa domin ceto jihar Kano daga tuƙin-tsayen ƴan tsiya-tsiya.
Kuma gashi hakan shine ya faru. Ƙuri'a miliyan ɗaya da ɗoriya da Madugu ya samu a Kano, itace ta samar mana da sanatoci mutanen ƙwarai guda biyu, tare da rinjaye a kujerun majalisar tarayya da najiha, har ma da kujerar gwamnan kacokam.
Idan son zuciya ne, Madugu zai iya karɓar tayin Peter Obi, su jone su mulki Nijeriya tare. Na san mutane zasu ce ai ko an haɗe ƙuri'unsu wuri guda ba zasu kamo na Tinubu ba. Amma kuma ai yawancin mutanen da basu yi zaɓe ba sun ƙi yi ne saboda suna ganin babu ƙwaƙwƙwaran wanda zai iya kada jam'iyya mai mulki. Wanda kuma haɗewar Ƙwankwaso da Obi zata iya samarwa da ƴan kan katanga ƙwarin gwiwar yin zaɓe. Haka ma Kwankwaso zai iya zamansa a PDP, ko ya koma APC domin kwaɗayin wani abu. Amma duka hakan zai samar masa da mafita shi kaɗai ne kawai, su kuma al'ummar Kano a barsu a hannun ƴan zari-zuga. Amma sai ya sadaukar da duk waɗannan damarmaki, ya biyo hanyar da zata ceci mutanen Kano, koda kuwa bayan zaɓe shi zai zamo bashi da kujera ko muƙamin komai.
A taƙaice, ya kamata mutane su gane cewar ɗaya daga cikin dalilan da Ƙwankwaso ya fito takarar shugaban ƙasa shine domin ya ceto siyasa haɗi da gudanar da mulkin Kano. Su kuma mutanen Kano sun zaɓi Ƙwankwaso a zaɓen shugaban ƙasa ne domin su ruguza alkadarin mutanen da suka lalata siyasar Kano, saboda ta hanyar zaɓen jam'iyyar NNPP ne kaɗai zasu firgita masu tunanin zasu iya kawo naƙasu wurin kafuwar sabuwar gwamnatin cigaba. Idan babu Ƙwankwaso a tikitin shugaban ƙasa, kuma idan mutanen Kano basu zaɓe shi ba, abune mawuyaci a samu sauyin sanatoci da ƴan majalisu. Idan kuma ba'a samu sauyin ƴan majalisu da sanatoci ba, cin kujerar gwamna zai zama kamar abinda ba zai yiwuwu ba ma.
Me yiwuwa wasu zasu ce, shin ku ƴan Kano kun gwamma ce kenan ku farfaɗo da siyasar Kano akan ku tallafawa ɗan Arewa (Atiku) ya zamo shugaban ƙasa? Amsar kuma itace eh, tabbas a kan ƙadamin da ake kai, farfaɗo da siyasar Kano ya fiyewa Bakano muhimmanci akan zamowar ko ma waye shugaban ƙasa. Hujja kuwa itace, idan jiha bata da gwamnati jajirtacciya, duk jajircewar gwamnatin tarayya zata tashi a banza. Amma kuma idan jiha tana da gwamnati jajirtacciya, duk lalacewar gwamnatin tarayya tana iya samun cigaba. Wannan wani ilimi ne da misalan gudanar da gwamnati a Nijeriya suka koyar damu.
A ƙarshe, idan mun yi laifi, muna roƙon ayi haƙuri. Duk da cewa dokar ƙasa tace babu buƙatar yin haka. Mun shiga wani yanayi ne da ya zamo tilas sai gida ya gyaru zamu fara hangen nesa. Kuma zaɓen da muka yiwa Madugu ya fara sanya tubalin yiwa siyasar Kano garanbawul. Allâh ya tabbatar mana da alkairi. Amîn.
MA Iliasu
20th March, 2023.
Comments
Post a Comment