(37):Me Yasa Ɗalibai Suke Cin Bashi Su Karanci Falsafa?
MA Iliasu. Ita ce tambayar da Tim Harford mawallafin littafin "Undercover Economist" ya yiwa kansa. Saboda na farko dai karatun falsafa ba kamar injiniyarin bane, da za'a yi amfani da fasaha a maida ƙarfe ya koma inji. Kuma ba kamar likitanci bane, da za'a fafe cikin mara lafiya ayi masa aiki ya miƙe. Kuma ba kamar lissafi bane, da za'a yi nazari a gano wani lokon kimiyya da babu shi ada. Kuma ba ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa bane, da za'a ƙirƙiri sababbin manhajojin kawo sauƙi a al'amuran yau da kullum. Kuma ba kamar lauyanci bane, da za'a gano muhallin doka don kama masu laifi a ƙundume kuma a wanke marasa shi. Kuma ba kamar bokon tattali bane, da za'a yi amfani da lissafi da ƙididdiga auna yawan ma'adanan da ake buƙata domin aiwatar da wata harka ko naƙalto abinda ke shirin faruwa. Kuma gashi dai falsafar nan bata maida sisi ya koma kwabo, a ƙalla dai ba a yadda muka sani kai tsaye ba. Kuma bata da wani muhalli da za'a ce gashi nan m...