(37):Me Yasa Ɗalibai Suke Cin Bashi Su Karanci Falsafa?
MA Iliasu.
Ita ce tambayar da Tim Harford mawallafin littafin "Undercover Economist" ya yiwa kansa. Saboda na farko dai karatun falsafa ba kamar injiniyarin bane, da za'a yi amfani da fasaha a maida ƙarfe ya koma inji. Kuma ba kamar likitanci bane, da za'a fafe cikin mara lafiya ayi masa aiki ya miƙe. Kuma ba kamar lissafi bane, da za'a yi nazari a gano wani lokon kimiyya da babu shi ada. Kuma ba ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa bane, da za'a ƙirƙiri sababbin manhajojin kawo sauƙi a al'amuran yau da kullum. Kuma ba kamar lauyanci bane, da za'a gano muhallin doka don kama masu laifi a ƙundume kuma a wanke marasa shi. Kuma ba kamar bokon tattali bane, da za'a yi amfani da lissafi da ƙididdiga auna yawan ma'adanan da ake buƙata domin aiwatar da wata harka ko naƙalto abinda ke shirin faruwa. Kuma gashi dai falsafar nan bata maida sisi ya koma kwabo, a ƙalla dai ba a yadda muka sani kai tsaye ba. Kuma bata da wani muhalli da za'a ce gashi nan masana'antar falsafa ce inda masana falsafa ke aiki kamar asibiti a gun likitoci, idan ka wuce makaranta inda masananta ke shiga malunta su koyar da ɗalibai.
A saboda haka wace kasassaɓar ce zata tunzura matashi yaci bashi yaje ya karanta wanna fagen ilimi mai matuƙar ruɗarwa, wahalarwa da cin lokaci, kuma mai rikitaccen muhalli a lamurran masana'antar yau da kullum?
Sai Mallam Harford yayi nazari ya gano cewa idan aka cire manyan fagen aiyuka da suke buƙatar gwanancewa ta musamman kamar likitanci, injiniyarin da lauyanci, aiki a Turai da Amurka a yanzu yakai wani matakin da babu abinda zai iya hana mutum yinsa sai ragwanta da sangarta. Wato matuƙar mutum jurarre ne, idan aka kaishi fagen, zai iya sunkwi da kansa ya koya, kuma ya iya, har ma ya zamo mashahuri a kansa. Sai ya bada misali da masana ilimin kasuwancin da suka tuba suka koma kimiyyar na'ura, da masana lauyanci da suka koma saye da sayarwa, har ma da masana injiniyarin ɗin da suka koma aikin banki.
Sai ya juya alƙalamin binciken ta hanyar cewa, yanzu ka ƙaddara ɗalibi ne yaje jami'a ya karanci falsafa, ya gama da matakin daraja ta ɗaya, shin a cikin idanunsa zaka iya gano sangarta ko son jiki?
A ra'ayin Harford hakan bazai yiwuwu ba. Saboda ta yaya ne wanda ya shafe shekaru biyar yana bita tun daga kan Socrates har zuwa Ferguson da Chomsky, yana nazarin azanci, hankali, tunani da aiki, sahihanci zance da ƙissime-ƙissime, ma'anar ciki da ta waje - ta hanyar karatu da rubutu tsababa, zance da tunani rututu - ta yaya za'a samu wannan da son jiki?
Wannan hujja, a mahangar Harford, ita mai kamfanin Microsoft zai kalla idan yana nazarin waye zai iya koyar aiki a sabon sashen aikin dake buƙatar ma'aikata. Kuma hujjarsa ta nuna hakan!
Digiri, maimakon abinda maƙaryata suke wallafawa, yafi auna aiki tuƙuru fiye da gogewa a wani fage. Saboda idan gogewa ce, ɗan kasuwa mai juya miliyan ashirin yafi mai digiri biyu a kasuwanci sanin menene kasuwa. Amma kuma tsakaninsu wanene zai iya fita daga harkarsa ya shiga wata ba tare da jin tsoro ba ko kuma har ma yayi nasara?
Abun nufi a nan shine, idan ƙaramin ɗan kasuwa mara ilimi ya fita daga kasuwa da nufin koyar wata sana'a sunansa nama. Saboda babu lallai ya iya koyar wata sana'ar da zaiji daɗinta kamar ta baya. Amma mai digiri a litirica zai iya fita daga koyarwa yaje ya koyi na'ura mai ƙwaƙwalwa ko ƙididdiga ko aikin jarida ya cigaba da ƙwamawa. Idan ma yaso zai iya ajiye komai a gefe ya tafi kasuwar ya koya har ya goge. Kenan mai ilimi yana iya koyar aikin mara ilimi ya goge amma mara ilimi iya aikinsa kaɗai zai iya?
Babu laifi idan mutane suka zaɓi abinda ke kawo kuɗi da wuri fiye da mai dogon zango, musamman a zamaninmu na jari hujja. Sai dai a daɗe a nayi sai gaskiya! Kuma mai arziƙi ko a kwara ya sai da ruwa, kuma ilimi shine tubalin arziƙi.
Jawabi na ga masu digirin da marasa digiri ke tsokana saboda sun fisu samun tagomashi shine, dagewarka itace jarinka. Babu wanda ya jure wahalallen karatun jami'a na tsawon shekaru huɗu da zaije wani fage ya kasa iyawa. Sai dai idan sangartaccen malalacine. Maras digiri bashi da wannan juriyar, saboda komai ya koya ya koya ne da kansa ko kuma bisa wani manhaji wanda babu tilastawa da togaciyya a ciki. Kimtsinku bazai taɓa zama ɗaya da kai da kake kaiwa ƙarfe biyun dare kana neman bayanai ba!
Shi yasa idan zaka bani dama dubu don yiwa mutane huɗuba abu na farko da zan faɗa musu shine su nemi ilimi da farko, so samu digiri a fagen kimiyya da fasahar zamani, ko kuma koma wane irin fage ne, sannan su shiga sana'a. Idan zasu iya biyun a tare su aikata hakan. Ilimi da sana'a abokan juna ne, ba maƙiya bane da basa ga maciji ba. Karhanta hakan rashin fuskantar kimiyyar al'amura ne!
Tuntuɓeni ta nan domin gyara da ƙarin jawabi: muhada102@gmail.com.
Wannan bayani yasa zan bukaci kayi wani rubutu akan halin da al'ummanmu ke ciki na fifita certificate akan hakikanin ilimin da ke makaranta.
ReplyDeleteAllah ya saka da alheri.
Masha Allah
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDelete