(35): Badaƙalar Maraya.

 MA Iliasu.

Wani abu dana koya daga rayuwa a aikace, wanda kuma bana zaton yawancin al'umma sun taɓa zama sun ayyana girmansa da tasirinsa ballentana suyi yunƙurin sauya al'adunsu na yau da kullum domin kawo masa maslaha shine yadda salon tunanin maraya ke canzawa bayan wafatin iyayensa koda kuwa majiɓinta al'amarinsa sun kasance jajurtattu.

Rayuwa gaba ɗayan ta ta ginu akan alaƙoƙi tsakanin mutane da al'amura daban daban. Musamman rayuwar yaro - wanda ƙanƙantarsa, kasawarsa da saurin gajiyawarsa suka sanya yafi kowane nau'i na ɗan Adam dogara akan alaƙoƙinsa da sauran mutane, musamman abinda ya shafi lura, tarbiyya, al'amarin zumunci da sauran alaƙoƙin ƴan uwa da dangi baki ɗaya. Tunanin maraya yana ginuwa bisa wani azanci na musamman, sakamakon wasu badaƙaloli da zan lissafo kuma na fayyace, wanda a aikace sune suka fi tasirantarsa.

Azanci na farko da tunanin maraya yake hawa shine zancen zuci wanda zai ringa ƙissima masa cewar tunda yanzu fa iyayensa basu da rai to ya zamo ɗan dangi mai daraja ta ƙasa, maimakon mai daraja ta sama a lokacin da walidansa ke da rai. Tunda dai wanene zai tsallake ɗansa ya fifita shi? A saboda haka komai ƙanƙantar canza fuska daga wurin ƴan uwa, koda anyi bada niyyar ƙuntatawa ba, tana samun ma'ana maras kyau a idanun maraya. Wato dai komai zai zamo kamar mai neman kuka ne a jefe shi da kashin awaki!

Azanci na biyu da tunanin maraya yake tafiya akai shine ya fara ƙissima cewa: "yanzu fa tunda ubanmu bashi da rai, maimakon mu taimaka sai dai mu a taimake mu". Don haka kulawar da za'a ringa bamu zata canza daga irin wadda ake bawa mai taimakawa zuwa kalar wanda ake taimaka. Daga wannan tunanin kuma sai al'amarin zumunci ya ɗauki wani salo kamar haka:

a) Maraya sai ya fara ɗari-ɗari da ƴan uwa - saboda yana jin tsoron kada ya shishshige musu wani yayi ƙorafin cewa maigida ya tafi ya barsu da aiki.

b) Maraya sai ya fara zumuɗin shishshigewa ƴan uwa - saboda yana jin tsoron kada ace daga mutuwar maigida ƴaƴansa sun dena shiga dangi.

c) Idan waɗancan tunaninnika masu cin karo da juna suka tararwa maraya a lokaci guda sai gaba ɗaya duniya ta haɗu tayi masa baƙiƙƙirin. Ya rasa ya zaiyi!

Azanci na uku da tunanin maraya yake tafiya akai shine yana fara tunanin ya za'ayi a idon danginsa ya kasance ba'ayi masa kallon gajiyayye ko kasashshe. Daga nan sai ya fara zille-zille. Idan mai zuciya ne sai ya kama sana'o'in ƙarfi, kalamansa su zamo masu cike da dagiya da musanta asalin me yake faruwa a cikin rayuwarsa. Duk don kada ayi masa kallon gajiyayye! Daga haka kuma idan aka yi rashin sa'a zai zamo ɗan dagiya har shekarun balaga.

Azanci na huɗu da tunanin maraya ke tafiya akai shine yana yunƙurin rarraba ƴan uwa da abokan arziƙi zuwa aji-aji. Inda matsalar take shine duk kusancin alaƙarku dashi (kawu, gwaggo, ƴan mazaa-zar, ƴan mata-zar, abokan wasa), idan baka da tsananin fara'a, maraya zai ajiyeka ne a ajin bare. Idan kuma kana da fara'a sosai, duk nisan alaƙarku, zai sakaka a ajin ƴan uwa na kusa. Sannan kuma maraya yafi so yayi alaƙa da ƴan uwa wanda yanayin rayuwarsu zaifi tuna masa da rayuwar da take fuskantarsa anan gaba, fiye da wadda ya baro a bawa (yawanci rayuwar wadata ce aka baro kuma akasin haka maraya yafi fuskanta a gaba). Zaifi nesanta kansa daga ƴan uwa masu hannu da shuni, saboda ƴan uwa masu kwaɗayi da rashin kamun kai sunyi ijma'in cewa kamar sukari suke a gun ƙuda, indai ka ganshi a wurin su kwaɗayi yaje.

Toh amma duk da cewa akwai yiwuwar shi maraya ba kwaɗayin yaje yi ba, sanadiyyar maraici ya sanya ana yi masa kallon me neman taimako, musamman idan aka ganshi a fadar wanda suke da ikon yi. Amma kuma idan ƴan uwa marasa iko ne, zaifi samun salama wajen alaƙa dasu saboda koda ance yaje kwaɗayi ne, an san babu abinda za'a je yiwa kwaɗayin. Kuma wane sokon ne zaije nema inda yasan bazai samu ba?

Daga nan idan aka yi rashin sa'a, musamman idan ana samun yawan mace-macen mazaje a cikin dangi, sai kaga zumunci yana ƙara ƙarfi tsakanin talakawa su kuma masu iko an barsu a gefe ga ƴan uwa kwaɗayayyu, duk da cewa mai yiwuwa babu laifin ko masaniyar masu ikon a ciki gaba ɗaya.

Azanci na huɗu da tunanin maraya yake tafiya akai shine tsantseni yayin mu'amalar yau da kullum. Idan yana da hankali sosai, sai aga ya rage giggiwa, musamman idan a cikin dangi akwai misalin wani fitinanne daya taɓa cin karo da ƙalubale duk da cewa ubansa yana da rai. A sannan maraya zai faɗawa kansa: "idan haka ta faru ga mai uba, ina kuma gani?" Shi yasa marayu masu zurfin la'akari suka kasance masu nesanta kansu daga haɗari, jan magana, ga kuma gudun zuciya. Suna da saurin bada haƙuri da tsumayin jiran umarni. Kuma idan ba'ai sa'a ba, akan wannan ɗabi'ar tunaninsu zai ginu har zuwa shekarun balaga. Kuma illolin wannan ɗabi'u yana iya haifar da rashin sanin ƴanci da mutuncin kai, rashin ƙwarin gwiwa, karsashi da yawan jiran umarni (kamar dai abinda ya faru da Morgan Freeman a cikin shirin wasan kwaikwayon Shawshank Redemption lokacin da ya kama aiki a shagon sayar da kaya ba'ada ya fito daga gidan Ɗan Kande bayan shafe shekaru kusa da hamsin).

Azanci na biyar da tunanin maraya ke tafiya akai kuma yafi alaƙantuwa da fami da kuma jin cewa rayuwa taci amanarsa, musamman idan yakai shekarun aure, takai ya kawo macen da yake so, amma su kuma waliyyansa suka ga rashin dacewar ya kasance tare da ita. Abinda zai fara zuwa ransa shine: waɗannan mutanen fa ba haka ubana yayi musu ba, hasalima su idan suka zo da batu har ɗan hasafin sadaki yake bayarwa, amma kuma ni zasu hanani wadda nake so? Daga nan komai zai ringa fitowa ne daga tantance mai babansa ya aikata dashi za'a aikata masa akasin haka? Kuma idan ba'ai da gaske ba daga nan sai ya zama ɗan tawaye, kuma me yiwuwa zumunci ya rushe. Duk da cewa akwai yiwuwar ƴan uwanne ke da gaskiya!

Wata babbar badaƙala tana haifuwa idan makaranta ta bukaci maraya yazo da ubansa. Rigimar shine babu wanda zai tambaya yaje ya wakilce fiye da sau ɗaya face sai yaji cewa kamar rayuwa taci amanarsa. A tunaninsa don me yasa sai ya roƙi wakilci bayan kowa ubansa na rawar gindi yake zuwa taron iyayen yara? Idan mai gudun zuciya ne, sai ya nesanta kansa daga laifin da zai janyo a nemi ubansa a makarantar. Idan maras gudun zuciya ne kuma daga ranar ya shiga rigima da ƴan uwa, musamman idan ba masu wadatar lokaci bane.

Hakana idan maraya na neman shawara da jagoranci zai ringa jin kokwanton shin abinda yake aikatawa daidai ne ko kuma akwai gyara. Na farko zaiji cewa mai yiwuwa ba daidai yake ba amma kowa ya zuba masa ido saboda tsoron kada a gyara masa yayi halin ƴan tasha. Ko kuma dai daidai yake amma an dame shi da yawan shawarwari don kawai a nuna an isa dashi.

Waɗancan nau'o'i da salon tunani guda biyar suna ɗaya daga cikin wasu dake tasirantar tunani, halayya da ɗabi'un yara wanda ALLAH (SWT) ya jarraba da maraici tun daga shekarun ƙuruciya.

Hakan ya sanya  rayuwa da iyaye, duk talaucinsu da rashin ikonsu, take da matuƙar fifiko akan rayuwar maraici, koda kuwa maigida ya tafi ya barwa marayun dukiyar da takai fan taɓa sama. Saboda ko ba komai, kasantuwar iyayen mutum a raye suna bashi kariyar azanci da ikon tunani mai tsaftar da zai bashi damar ya maida hankali akan sauran al'amura muhimmai kamar karatu, walwala da zumunci ba tare da zurfafa tunani wajen nemo amsoshin da tunaninsa bai kai wajen ba.

Daga haka zamu gane cewa iyaye garkuwa ne - duk rauninsu kuwa. Kuma ƙarin karsashi ne - koda kuwa gyartai ne. Zamansu a raye waraka ne daga ciwon tunani mai yaɗon mugunya - suna ƙarawa zumunci da mu'amala ƙarfi. Suna assasa sanin ciwon kai ga ƴaƴayensu, da kuma ƙwarin gwiwar fuskantar ƙalubalen rayuwa. Maraya duk yana rasa wannan. Kuma mafi akasari yana koyon dabarun zaman duniya ne aikace, babbar illar kuma shine akan titi, wanda abune mai matuƙar haɗari. Gane hakan sosai sai ga wanda ya taɓa rayuwar maraici. Shi hasa kullum addu'a ta ga yara ƙanana shine ALLAH (SWT) ya raya su da iyayensu cikin ƙoshin lafiya. Idan kuma sun zamo marayu, ALLAH (SWT) ya jiɓinci lamarinsu a matsalolin da idanu ke iya gani da kuma wanda basa iya gani. 

Haƙiƙa Shugaban Halitta SAW yayi gaskiya a lokacin da yayi mana wasiyya: "ku jiɓinci al'amarin maraya. Ku shafa kansa". Tsira da aminci su tabbata a gare SHI da AHALINSA, da SAHABBANSA, da duk wanda ya bisu da kyuatayi har zuwa ranar tonon asiri. Ameeen.

An rubuta: 27-01-2022

Zaku iya tuntuɓata a adireshin imel kamar haka domin gyara ko ƙarin jawabi: muhada102@gmail.com

Comments

  1. Tabbas na tashi cikin maraici.wannan shine gaskiyar magana wlh .Dan duk nayi experiencing wannan ababen.Allah yasaka maka da Alheri.

    ReplyDelete

Post a Comment