(44); ME YASA KANAWA MUKA ZAƁI ƘWANKWASO A ZAƁEN SHUGABAN ƘASA DUK DA MUN SAN BA ZAI CI BA?
Ga mutane gama-gari wanda ba su da komai face ƙawa-zuci, ra'ayi kaɗai ya isa dalilin zaɓa ko ƙin zaɓar kowanne ɗan takara. Amma ga mutanen da abinda ake zato daga gare su ya kere ƙawa-zuci, buƙatar yanke shawara a gwanance domin cimma wata manufa ya zamo kamar wajibi ne a mahanjar al'umma masu kamanceceniyar addini, al'adu, wurin zama da kishin juna kamar tamu ta Arewacin Najeriya. Da Dr. Rabi'u Kwankwaso ya fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar NNPP a zaɓen Fabrairun 2023, yawancinmu mun san cewa fandishon jam'iyyar NNPP bai kai taci kujerar shugaban ƙasa ba. Hasalima Atiku Abubakar zai fi jam'iyyar samun yawan ƙuri'u. Idan kuma haka ne, zaɓar jam'iyyar, ko kuma kira da a zaɓi jam'iyyar, ai ya zama daidai da sanya jari a bankin asara kenan. Ko ba haka ba? Amma inda gizo ke saƙar shine, Kanawan Dabo sun zauna sun yi karatun ta natsu. Daga hakan kuma muka iya gano cewa jagora Kwankwaso yayi nazarin wasu daga cikin dalilan da suka janyo s...